@daboalherine8: "Zabin da ya fi wahala ba koyaushe ba ne wanda yake tsakanin abu biyu ba, wani lokacin yana tsakanin abin da kake so da abin da ka san ya dace."Wani lokacin abin da ya fi karya mana zuciya ba wai rashin samun abin da muke so ba ne, sai dai sanin cewa abin da muke so din ba shi ne abin da ya dace da mu ba. Zuciya tana iya jan mutum zuwa inda yake so, amma hankali yana tunasar da shi inda ya kamata ya dosa. Kuma a irin wannan lokacin ne ake gane cewa wasu zabukan ba sa bukatar karfin hali, suna bukatar ka iya barin abin da kake so saboda abin da ka san zai fi maka alheri.