@missionpodcast1: Dinki da Cigaba Podcast” Taken tashar: “Fadakarwa, dabaru da ci gaban masu sana’ar dinki da fashion. 1-Yawancin masu sana’ar dinki da fashion designers da ke gudanar da kasuwancinsu a matakin gida ba sa samun isasshen bayani kan dabarun zamani da za su taimaka wajen bunƙasa sana’arsu. Saboda haka, an gabatar da wannan podcast a matsayin mafita (solution) domin fadakarwa, ilmantarwa da ƙarfafa su su rungumi hanyoyin ci gaba. 2-Manufofin podcast ɗin: 1- Fadakar da teloli da fashion designers kan muhimmancin zamani a sana’arsu. 2-Koyar da dabarun gudanar da kasuwanci. 3- Bayar da shawarwari kan tallata sana’a ta yanar gizo. 4-Tattaunawa da mutanen da suka yi nasara a fannin. 5-Bayarda shawari da Koyar da yadda ake kula da kwastomomi da gina suna mai kyau ta hanyar alaqa.