A’I’B GLOBAL ENTERPRISES LTD :
Ya Allah, ina cikin bashi mai yawa, kuma damuwar bashin nan ta hana ni bacci wallahi. 😭🤲 Ya Allah, kai ne mai sauƙaƙa wahala, ina roƙonka da rahamarka, ka hore min hanyar biyan bashina.
Ya Allah, duk wanda ake bin bashi, ka hore masa abin biya, ka yaye masa damuwa, ka buɗe masa ƙofofin arziki na halal. Ya Allah, ka mayar mana da farin ciki bayan damuwa, ka ba mu mafita ta alheri, ka sa mu biya bashin da ake bin mu, ba tare da ƙasƙanci ko wahala ba.
Ya Allah, kada ka bar mu da nauyin bashi, ka sauƙaƙa mana al’amuranmu, ka ba mu kwanciyar hankali da natsuwar zuciya. Amin ya Rabbal Alamin. 🤲😭
2026-10-19 23:47:36