@uss21multimedia: Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Tinubu ya nemi afuwar ’yan Najeriya kan tsadar rayuwa da gwamnatinsa ta jefa Najeriya a ciki. Atiku ya bayyana hakan ne cikin sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ADC, Phrank Shaibu ya fitar. Ya ce cire tallafin man fetur da karya darajar naira sun ƙara tsadar abinci, sufuri da makamashi, inda ya buƙaci gwamnatin tarayya ta yi cikakken bayani kan yadda bashin ƙasar ya karu zuwa tiriliyan ₦166.79,#creatorsearchinsights #viralvideo #endbadgovernanceinnigeria #nigeriantiktok🇳🇬