@callme_majidadinmusabaq: INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN 😭💔 🕊️ HAFIZAR ALƘUR’ANI MARYAM ABUBAKAR ALIYU TA RASU YAYIN ƘOƘARIN CETON ƘANENTA Wani labari mai matuƙar ban tausayi ya riski al’ummar Mahaddata Alƙur’ani, bayan rasuwar Hafizar Alƙur’ani, Maryam Abubakar Aliyu, yayin da take ƙoƙarin ceton ƙanenta guda biyu da suka faɗa cikin ruwa. Maryam Abubakar Aliyu ta kasance daga cikin masu haddar Alƙur’ani, inda iyayenta suka turo ta daga Abuja zuwa Kano, tare da malamarta, domin ta samu damar haddace Littafin Allah Mai Girma. Sai dai cikin wani lamari mai matuƙar raɗaɗi, Maryam ta gamu da ajalinta a cikin ruwa yayin da take ƙoƙarin ceton ƙanenta guda biyu da suka faɗa cikin ruwa a bayan gidansu da ke Abuja. Abin takaici, ƙoƙarin ceton nasu bai yi nasara ba, inda Maryam da ɗaya daga cikin ƙannenta suka rasa rayukansu cikin wannan mummunan lamari. Wannan rashi ya kasance babban abin alhini, musamman idan aka yi la’akari da irin sadaukarwar da iyayenta suka yi wajen turo ta Kano domin ta samu damar haddace Alƙur’ani Mai Girma. A cewar malaminta, wanda ya tabbatar wa Ahlul Qur’an TV faruwar wannan al’amari, har zuwa wannan lokaci ba a samu nasarar gano gawar Maryam Abubakar Aliyu ba. 😭💔 Allah Ya jiƙan Maryam da rahama, Ya gafarta mata da ƙanenta, Ya sanya Alƙur’ani ya zama ceto gare su, Ya haskaka kabarinsu, Ya kuma ba iyalansu, malamansu da dukkan waɗanda wannan rashi ya shafa haƙurin jure wannan babban rashi. Ya Allah, ka karɓe su cikin rahamarka. 🤲🏽 Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
MAJIDADIN MUSABAQAH TV
Region: NG
Saturday 03 October 2026 12:58:52 GMT
Music
Download
Comments
BIGG-MANN :
May her soul rest in peace 🥹🙏
2026-10-03 17:17:24
0
al noor collection hub :
ameen ya rabbi
2026-10-03 20:33:40
0
JAJI :
Wlh a anguwanmu Take. Allah yajikanta
2026-10-03 17:32:21
34
oni musty :
May ALLAH grant her Jannah. Ameen
2026-10-03 14:06:50
67
Hayaa By Haajar 🧕🦋 :
May jannah be her final destination
2026-10-03 20:23:15
0
user8063592999718 :
May Almighty Allah grant her jannatul firdaus
2026-10-03 16:27:34
10
Fatima Jafar :
Allah ya jikanta yasa aljanna ce makomar ta ameeen thumma ameeen
2026-10-03 13:52:25
15
Zainab Gokaru :
Allah Ya mata rahama 🤲
2026-10-03 13:38:41
18
Speechless Jaybee :
may Allah grant her Jannah
2026-10-03 17:01:26
4
yariman Rigasa,🤲💴💯 :
ameen summa ameen 🤲🤲🤲😭
2026-10-03 20:31:43
0
A..B..B..k :
ameen thuma Ameen 🥰🥰🥰
2026-10-03 13:41:05
1
ouzeifa Issa Kane :
Allah jikan muslmi
2026-10-03 17:59:25
1
S◎ulSүn¢.001 ✅ :
Ameen ya hayyu ya qayyum 😭😞
2026-10-03 15:30:24
4
lailaskitchen :
Allah yajikanta darahama 😭
2026-10-03 16:30:13
5
𝖠v𝖽𝗈𝗅𝗅.𝗃𝗇𝗋🏝️ :
Masha Allah Allahumma bareek 🙏👏
2026-10-03 13:46:03
5
Anas Ibrahim :
Allah ya miki Rahma ya sa kin huta, wallahi kinfi Wanda zai mutu yana rawan TikTok
2026-10-03 20:23:42
0
idrees aleeyou lame :
ameen
2026-10-03 17:20:38
3
Abubakarmsa :
Innalillahi wa Innailaihi Raji'uuun Allah ya mata rahama yasa mutuwa hutuce a garemu gaba daya 😭
2026-10-03 16:06:47
6
zulaihaanas833 :
ameen ya Allah
2026-10-03 14:12:25
1
souleymaneguiro7 :
Qu’ALLAH lui fasse Miséricorde et l'accueille dans Son Immense Paradis
2026-10-03 19:31:40
2
MrMamzz :
Qanin nata ma ya rasu tare da ita ne?
2026-10-03 17:57:13
4
𝐌𝐔𝐒𝐀𝐇 𝑴 𝗦𝗔𝗟𝗔𝗛💯 :
amen
2026-10-03 13:49:41
4
hauwa u :
Allah yjknt
2026-10-03 17:11:41
2
Ameerah50 :
Allah sarki Allah ya mata rahma 😭
2026-10-03 15:24:40
1
2030🕋⛴️👳 :
May Allah grant her jannah 🤲🤲
2026-10-03 17:45:54
5
To see more videos from user @callme_majidadinmusabaq, please go to the Tikwm
homepage.