GIDAN TILES NDH COMPLEX :
*HUDUBAR JUMU'A AKAN: "KA TUNKUDE MUMMUNA DA WADDA TA FI KYAU" DAGA IMAM RAYYANU DAUDA PAMBEGUA ESQ*.
JUMUAH 21-4-1448AH/ 2-10-2026M.
*HUDUBA TA FARKO*
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Ya Allah gare Ka ne godiya mai yawa, mai kyau, mai albarka, godiyar da take cika ni'imomi kuma take saka karin ni'ima.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, ba Ya da abokin tarayya. Ina shaidawa cewa Shugabanmu, Annabinmu, masoyinmu Annabi Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa. Ya Allah ka yi salati, ka yi sallama, ka yi albarka a gare shi da iyalan gidansa da sahabbansa, sallama mai yawa.
Bayan haka, ya ku Musulmai masu daraja, lallai Allah Mai Gaskiya Mai tsarki Yana cewa a cikin littafinsa mai karamci:
*"Kyakyawa da mummuna ba daidai suke ba. Ka tunkari (mummuna) da wadda ta fi kyau. Sai ga shi wanda a tsakaninka da shi akwai gaba, sai ya zama kamar masoyi na kut-da-kut. Kuma babu wanda ake ba shi wannan dabi'a sai masu hakuri, kuma babu wanda ake ba shi sai mai rabo mai girma."* [Fussilat: 34-35]
'Yan uwa musulmi, lallai Shari'ar Musulunci ba ta zo don ta tsara alakar bauta tsakanin bawa da Ubangijinsa kadai ba, a'a ta zo ne domin ta gina al'umma da ke daure da juna bisa tubalin dabi'u madaukaka da tsarkin zuciya.
A cikin wani zamani da rigingimu suka yi yawa, mutane suka rika yin sauri wajen mayar da martani da misalin mummunan da aka yi musu, hatta ma da karin muni, sai umarnin Alkur'ani ya zo, ya zana mana hanya ta Ubangiji kebantacciya, wato hanyar *"Ka tunkude mummuna da wadda ta fi kyau."*
Tunkude mummuna da wadda ta fi kyau wata ka'ida ce mai girma, ba rauni ba ce kuma ba zabin raunana ba ne, a'a ita ce kololuwar karfin zuciya, kuma nasara ce da hankali da imani suka yi a kan tabaibayin Shaidan. Ita ce hanya daya tak da za ta mayar da gaba zuwa abota, ta mayar da tsauri zuwa laushi, ta mayar da sabani zuwa aminchi.
'Yan uwa masu imani, wannan hanyar ta *"Idfa' billati hiya ahsan"* an umurce mu da ita a cikin dukkan sha'anin rayuwa:
*1. A wajen fuskantar cutarwar mutane:* Allah Mai Rahama Yana cewa: *"Ka tunkude mummuna da wadda ta fi kyau. Mu ne Mafi sani da abin da suke siffantawa."* [Al-Mu'minun: 96]
Mumini baya may
2026-10-06 11:42:13