@hdacter.u3: 🚨🔥 DA DUMI-DUMI: KADUBA GAGGAMIN TARON ADC A JIHAR ZAMFARA A DAREN NAN! An gudanar da wani babban taron magoya bayan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Zamfara a daren yau, inda aka ga dimbin jama’a da magoya bayan jam’iyyar sun hallara. Taron na zuwa ne yayin da jam’iyyar ke ƙara ƙarfafa shirye-shiryenta gabanin zaɓen 2027, tare da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC. A yayin tarukan da suka shafi ADC a baya-bayan nan, taken “Tinubu Must Go” ya kasance ɗaya daga cikin kalaman siyasa da magoya bayan wannan yunƙuri ke amfani da su. Atiku ma ya bayyana goyon bayansa ga wannan ƙungiya a watan Satumba. 📸 Kalli hotunan taron na daren nan… #ADC #AtikuAbubakar #Zamfara #TinubuMustGo #H_DacterU3