U tubalin s doka ✅ :
CP Usman Shugaba CPSO Zeyi Bacci Cikin Salama Acikin Jama'arsa Ko Bayan Ya Gama Aiki!
Shugaba ya samu dama, kuma yayi amfani da damar ya gina mutane, ya inganta yankinsa da mazaɓarsa. Irin matasan da shugaba ya gina ko bayan ba ransa iyalansa bazasu wofanta ba, hatta nakusa dashi bazasu wulaƙanta ba. Ya gina mutane batare da tunanin sakayya ko neman komai daga garesu ba.
Wannan shine dalilin da yasa ya zama kamar kuɗi acikin unguwarsa, duk sanda akace ya shigo gari kullum cikin ganin mutane yake, kowa rububin ganinsa yake saboda ya taɓa yimasa wani alkairi a baya, ko kuma saran zeyi masa wani alkairi a gaba. Batare da tsoro ko firgici ba yake shiga kowanne lungu, kowanne gida dake yankinsa, domin yasan abun alkairi ya shuka ba abun tsiya ba.
Rayuwar shugaba babban darasi ce ga sauran ƴan siyasa wanda suke da dama a hanunsu, koda ace samu ko matsayinka bekai na Shigaba ba, duk da haka zaka'iya taimakon mutane dai-dai ƙarfinka. Domin abinda ka ajiye ayau, shi zaka ɗauka a gobe. Wallahi duk abinda ka shuka shi zaka tarar. Za'a daɗe ba'a manta da shugaba ba, kamar yadda haryanzu al'ummar tudun wada suka kasa manta Alhaji Ahmadu Chanchangi.
Duk wanda ya samu dama ya taimaki mutane, ko talauci ya riskeshi iyalansa bazasu taɓa tozarta ba. Rayuwar shugaba abar koyi ce musamman garemu matasa, Allah kabamu damar, sannan kabamu ikon taimakon mutane kafin damar tabar hanun mu🙏🏿!!!
U Tubalin S Doka ✍️✍️✍️
2026-10-17 13:07:46