@trtafrikaha: Jiragen ruwa biyu sun nutse a kusa da Hormuz yayin da hare-hare suka karu Jirgin ɗaukar kwantena da wani jirgin ɗaukar busassun kaya sun nutse kusa da Mashigar Hormuz cikin sa’o’i 24 da suka gabata, bayan wasu makamai sun same su a hare-hare daban-daban, a cewar jami’an harkokin ruwa a ranar Laraba. An bayar da rahoton ɓacewar ma’aikatan jirgin ruwa biyu. Bayanai kan tsaro sun nuna cewa an kai wa aƙalla jiragen ruwa 10 hari a kusa da Mashigar Hormuz tun ranar Lahadi, adadin da ya fi na kowane lokaci tun bayan fara yaƙin Amurka da Isra’ila da Iran. Majiyoyin tsaron teku sun ce jirgin GFS Pride, mai ɗauke da tutar Singapore, ya nutse ne yayin da yake wucewa ta mashigar. Rundunar sojojin ruwa ta dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran ta ce jirgin ya nutse ne bayan ya taka nakiya. A wani hari na daban, jirgin Cape Dao, mai ɗauke da tutar Antigua da Barbuda, ya nutse kusa da mashigar makonni bayan wani makami ya same shi a ranar 23 ga Satumba. Hakan na cikin bayanan da Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Ruwa ta Duniya (IMO), ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya, ta wallafa a ranar Laraba. An samu rahoton hare-hare 23 tun farkon watan Oktoba, kusan ninki biyu na matsakaicin hare-haren da ake samu a kowane wata tun bayan fara yaƙin. A cewar IMO, kusan ma’aikatan jiragen ruwa 24 ne suka mutu a hare-hare da sauran al’amura a yankin mashigar Hormuz tun bayan barkewar rikicin.
TRT Afrika Hausa
Region: NG
Thursday 15 October 2026 19:45:00 GMT
Music
Download
Comments
ismail atamfawa :
welcome to comment section ti okofi😅
2026-10-15 19:47:44
0
Oga Gaddafi :
[Pray][Pray][Pray][Pray][Pray][Pray]
2026-10-15 19:52:57
0
To see more videos from user @trtafrikaha, please go to the Tikwm
homepage.