@adn.hausa2: Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan wasu ’yan ƙasar Bangladesh biyu da aka samu da laifin aikata badala a cikin masallacin Harami da ke birnin Makka. Wata jaridar Khaleej Times ta ruwaito cewa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, inda ta bayyana sunayen mutanen da aka kashea a matsayin Nazrul Islam Abdul Basir da Siti Akhtar. Ma’aikatar ta ce jami’an tsaro sun kama mutanen biyu bayan faruwar lamarin, inda aka gudanar da bincike tare da gurfanar da su a gaban kotun da ta dace. Daga bisani, kotun ta same su da laifi, ta kuma yanke musu hukuncin kisa bisa la’akari da girman laifin da kuma keta alfarmar lokaci da wurin da abin ya faru. Sanarwar ta bayyana cewa an yanke musu hukuncin ne ƙarƙashin tsarin **Ta’azir**, wanda ke ba kotu damar yanke hukuncin ladabtarwa bisa tanade-tanaden Shari’ar Musulunci. Ma’aikatar ta ƙara da cewa hukuncin ya zama na ƙarshe bayan hukumomin da abin ya shafa sun tabbatar da shi. Daga nan ne aka bayar da umarnin sarauta na aiwatar da hukuncin kisan bisa Shari’ar Musulunci. Sanarwar ta ce an aiwatar da hukuncin kisan ne a yankin Makka a ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026. Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta sake jaddada ƙudurin gwamnatin ƙasar na tabbatar da tsaro, tabbatar da adalci da kuma aiwatar da dokokin Shari’a kan duk wanda ya karya alfarmar masallatai ko ya aikata laifukan da suka shafi mutuncin wasu. Ta kuma yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da aikata irin waɗannan laifuka zai fuskanci hukuncin da Shari’ar Musulunci ta tanada.

ADN HAUSA
ADN HAUSA
Open In TikTok:
Region: NG
Monday 19 October 2026 21:56:54 GMT
40285
1449
41
112

Music

Download

Comments

abdoulkarim0900
isaktan toumass :
yayi dayday
2026-10-20 06:55:55
1
usmanabubakarsark4
usmanabubakarsark4 :
akasesu
2026-10-20 09:43:27
1
abdoulmadjidzabei
Abdoul Madjid Zabeirou Assouma :
yayi daiday
2026-10-20 07:06:14
1
nazifi.adamu15
Nazifi Adamu :
yayi dede
2026-10-20 12:54:25
0
salisumusa2685
salisu :
yayi daidaye
2026-10-20 14:02:13
0
user623139282330
Ibirahim muhammeed :
@u@
2026-10-20 16:06:07
0
nuratanimun5
BACHIR ALI 13 agadez :
akachesu
2026-10-20 09:26:00
1
zaya69989
zaya :
🥰🥰🥰
2026-10-20 12:01:49
1
bellaprou
Bella💘💘💘🥰🥰proU :
👍👍👍👍👍👍👍
2026-10-20 09:48:27
1
ibrahim.mss19
DAHIROU..LIDO :
👍👍👍
2026-10-20 09:14:27
1
harouna.attri
22 :
🥰🥰🥰
2026-10-20 05:49:52
1
nasrinsani928
nisirin sani k3 :
👍👍👍👍
2026-10-20 11:25:50
1
mammansanigomna11
M. Sani gwamna 🇳🇪A🇲🇱E🇧🇫S :
♥️♥️♥️
2026-10-20 10:12:52
1
zainab.abu580
zainab Abu :
@👍👍👍
2026-10-20 11:28:26
1
aminou.asoumana35
Aminou Asoumana :
🥰🥰🥰
2026-10-20 16:25:13
0
maman.lawali123
Maman Lawali :
🥰🥰🥰
2026-10-20 15:02:57
0
rabe.abab2
Rabe Abaa :
🥰🥰🥰
2026-10-20 16:12:44
0
user36p2jclpp2
jamila :
👍👍👍👍
2026-10-20 12:01:08
0
abduijjjh
abduijjjh :
🥰🥰🥰
2026-10-20 13:52:15
0
adam.dabaga7797
adam dabaga7797 :
[En larmes][En larmes][En larmes]
2026-10-20 13:46:41
0
aliyu.manman78
Aliyu Manman :
[Big LOL][Big LOL][Big LOL]
2026-10-20 12:21:01
0
user7702968981
Ibrahim Muhammad :
👍👍👍👍👍
2026-10-20 13:27:17
0
fauziyaumar3618
Fauziya Umar :
🤜🤜🤜🤜🤜👍👍👍
2026-10-20 18:29:13
0
youssif4865
Youssif :
😳😳😳
2026-10-20 11:59:02
0
user2096908523469
على حسين :
🥰🥰🥰
2026-10-20 05:14:02
1
To see more videos from user @adn.hausa2, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos


About