Teemah Mai tsada :
Wallahi, duk ranar da aka biya mini Umrah, na rantse da Allah, farin cikin da zan ji ba zai bar ni in iya bacci ba. 😭🤲❤️Ya Allah, ina roƙonKa da sunayenKa mafi kyau, Ka sanya ina da rabon zuwa Umrah. Duk da cewa ban ajiye kuɗi ba, kuma ban ba kowa kuɗi ya ajiye mini ba, amma Ya Allah, Kai ne Mai ikon yin abin da babu zato, babu tsammani.
Ya Allah, Ka yi mini ta inda ban yi tsammani ba. Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa, Ka azurta ni da kuɗin zuwa Umrah ta hanya mafi alheri. Ya Allah, Ka sa in ga Ka’aba da idanuwana, in yi addu’a a gabanta, in zubar da hawayen farin ciki a ƙasa mai tsarki.
Ya Rabb, idan akwai wanda za Ka ba shi damar zama sanadin zuwa na Umrah, Ka sa ni cikin waɗanda za Ka zaɓa. Ka kawo mini taimako daga inda ban yi zato ba, Ka sa mafarkina ya zama gaskiya, Ka kuma sa ranar da zan samu labarin an biya mini Umrah ta zama ranar da ba zan taɓa mantawa da ita ba.
Ya Allah, ina da buri, ina da fata, kuma ina da Yaƙini da ikonKa. Ba ni da kuɗi a hannu, amma ina da Ubangiji Mai arziki, wanda idan Ya so abu, sai ya kasance.
Ya Allah, kada Ka bar ni da burina kawai. Ka cika mini shi da rahamarKa, Ka rubuta mini rabon zuwa Umrah cikin sauƙi, lafiya da albarka.
Ameen Ya Rabbal Alameen. 🤲😭❤️🕋
2026-10-23 11:48:03