Barka da wanan lokaci cikakkiyar rabin rayuwata, farin cikin zuciyata, kuma ginshiƙin farin cikina. 💋❤️Ina fatan kin tashi lafiya, masoyiyata. 🥰❤️Allah Ya sa wannan safiyar ta zo miki da alheri, farin ciki da kwanciyar hankali. Kin kasance cikin tunanina tun kafin na buɗe idanuwana, domin ke ce hasken da ke haskaka rayuwata. 😘💞
Ina roƙon Allah Ya kiyaye min ke, Ya tsare min murmushinki, Ya sa farin ciki ya zama abokin rayuwarki a kowane lokaci. ❤️🌹
Ki sani, masoyiyata, duk ranar da na tashi ina tuna da ke, ranar ce ta fara min da albarka. Ina matuƙar ƙaunarki, sarauniyar zuciyata. 💋❤️😘