@firstladytalks: Ba wai muna neman namiji marar kuskure ba ne, amma akwai wasu halaye da bai kamata mace ta yi watsi da su ba saboda kawai tana son mutum. Kada ki duba yadda yake nuna miki soyayya kawai, ki duba yadda yake mu’amala da ke idan ya yi fushi, yadda yake girmama ki, yadda yake ɗaukar alhakin kuskurensa da yadda yake mutunta sauran mutane. Ka tuna: Ba duk namijin da yake son ya aure ki ba ne yake da halayen zama miji nagari. Allah Ya ba mu zabin nagari. Ameen. ❤️