@sirrinso3: 💌 WASIKAR SOYAYYA ❤️🥀 Masoyiyata, ba sai na gan ki a kullum ba kafin in tuna da ke. Domin kin zama wani ɓangare na tunanina. Duk lokacin da na tuna da ke, zuciyata tana samun wani irin farin ciki na musamman. Ina son mu zama masoya masu gaskiya, waɗanda ba sa gajiya da fahimtar juna. Ina son mu riƙe amana, mu yafe wa juna, kuma mu kasance tare cikin farin ciki da ƙalubale. Ba na neman soyayya ta yau da gobe, ina neman soyayya mai ɗorewa wadda za ta zama abin alfahari a rayuwarmu. Allah Ya sa mu zama alheri ga juna. ❤️🔐💍