@rfi_ha: Kowane ɗan Kaduna ana bin sa bashin fiye da naira dubu 90 - Usman Bawa Ɗan takarar Gwamnan Kaduna na jam'iyyar PDP, Usman Bawa ya ce ana bin ƴan jihar bashin fiye da naira dubu 90 kowane mutum guda sakamakon basussukan da gwamnatin Nasir El-Rufai da ta gabata ta ciyo, da kuma na gwamnati mai ci ta Uba Sani. Yayin hirarsa da wakilin RFI Hausa, Aminu Sani Sado, ɗan takarar ya bayyana irin ƙudurorin da yake dasu na kawo ci gaban jihar idan ya yi nasara a zaɓen 2027.