Allah Ubangiji Ya shiryar da ke, Ya buɗe zuciyarki ki gane gaskiya, Ya haskaka miki hanyar da ta dace, Ya nisantar da ke daga duk abin da ba shi da alheri a gare ki. Allah Ya ba ki ikon bambance gaskiya da ƙarya, Ya sa ki karɓi gaskiya ko da tana da ɗaci. Ina roƙon Allah Ya gyara zuciyarki, Ya albarkaci rayuwarki, Ya kuma shiryar da mu baki ɗaya zuwa ga tafarki madaidaici. 🤲🤲