@abba_bloger: Fitaccen malamin ɗariƙar Tijjaniyya a Kano, Malam Muhammad Nura Arzai Aujara, ya ƙalubalanci Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan ziyarar Umrah da ya gudanar a ƙasa mai tsarki ba tare da kai ziyarar Annabi Muhammad (S.A.W.) a Madina ba. Malam Arzai Aujara ya bayyana cewa shugaban ƙasar ya yi musu babban laifi, bisa rashin kai wannan ziyara. A rahoton da fadar shugaban ƙasa ta fitar, an tabbatar da cewa Tinubu ya kammala Umrah a Makka tare da barin Saudiyya ranar 4 ga Nuwamba, 2026. Sai dai ba a bayyana batun ziyarar Madina a sanarwar ba. #Tinubu #MuhammadNuraArzaiAujara #Umrah #Tijjaniyya #NigeriaPolitics