@premierradiong: Iyalai da kungiyar al’ummar musulmi mabiya Alkur’ani ta Najeriya karkashin jagorancin Sheikh Malam Usman Dangungu Kaduna, sun bayyana cewa suna dakon sakamakon binciken hukumomin tsaro kan kisan Marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka kafin daukar mataki na gaba. Daya daga cikin manyan almajiran shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Yunusa Abdulkadir Mai-Risala Kano, ya bayyana cewa ba za su taba yafe wannan danyen aiki da ya kira na ta’addanci da take hakkin dan’adam ba. Malamin ya jaddada cewa kungiyar a shirye take ta dauki kwararan matakan shari’a a kan duk wanda binciken hukumomin tsaro ya kama da hannu a kisan malamin ba tare da sassauci ba. Dangane da ikirarin da kungiyar Ansaru ta yi na cewa ita ce ta kashe malamin kuwa, Sheikh Mai-Risala ya bayyana hakan a matsayin wata dabara ce kawai ta dauke hankalin al'umma daga ainihin wadanda suka aikata wannan kisa. Sheikh Yunusa Mai-Risala ya bayyana hakan ne a yau Asabar a birnin Kano, yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai dangane da halin da ake ciki kan kisan malamin.