@ibrahim_sheriff_aminu: A rayuwa, ba duk abin da kake nema ne zai zo a lokacin da kake so ba. Wani lokaci za ka yi ƙoƙari, ka sadaukar da lokacinka, ka sha wahala, amma sakamakon da kake fata ya ƙi bayyana. A nan ne mutane da yawa suke fid da rai, ba don sun kasa ba, sai don sun gaji da jiran abin da suke ganin ya kamata ace ya zo. Amma ka fahimta : Jinkirin samun nasara ba yana nufin ƙoƙarinka ya tafi a banza ba ne. ⏳ Haƙuri ba wai zama kawai kana jiran al'amura su canza ba ne; haƙuri shi ne ci gaba da yin abin da ya dace, ko da kuwa ba ka ga sakamakon ƙoƙarinka a yanzu ba. Kada ka bari saurin nasarar wani ya sa ka raina tafiyarka. Kowa yana da lokacinsa, amma ba kowa ne yake da ƙarfin jurewa har zuwa ƙarshen tafiyarsa ba. Ka tuna, haƙuri shi ne gadar da ke haɗa ƙoƙari da nasara. Wanda ya gaji ya tsaya, wataƙila abun da yarage masa mataki ɗaya kacal ya isa inda yake mafarki. 🖤 Ba dole ne ka yi sauri ba, amma kada ka daina tafiya. 🌿 Ka ci gaba da ƙoƙari, domin bishiya idan tana girma ba a ganin jijiyoyin ta Allah yabamu dacewa 🤲 #foryou #capcut #arewa__tiktok #ibrahim_sheriff_aminu #fyp

🅢🅗🅔_🅡🅘🅕🅕 🧑‍✈️
🅢🅗🅔_🅡🅘🅕🅕 🧑‍✈️
Open In TikTok:
Region: NG
Saturday 07 November 2026 22:12:10 GMT
4304
482
5
7

Music

Download

Comments

itzmuhammd
muhammed saddam :
thank u brotheru🥰🥰🥰
2026-11-08 21:29:00
0
hallarou02
HallarouⓂ️ :
tabbas
2026-11-08 16:40:49
0
junior__kano
Sagir_Bin_Said 🇳🇬 :
"Haquri shine gadar" dake hada "ko"kari da nasara 😏
2026-11-08 17:26:13
0
axxamphary
🦅📉AXXAMPHARY📉🦅 :
My goal is to surprise myself one day
2026-11-08 07:03:00
0
To see more videos from user @ibrahim_sheriff_aminu, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos


About