@abdullahiabubaka57:*ALAMOMIN TASHIN KIYAMA - 20*
HAKA KAWAI na tashi naji anata kara jita jita akan duniya zata tashi wannan juma.a sainayi amfani da wannan damar domin tunatar damu alamomin tashi kiyama kar wasu su rudemu daga abduldmainera
*1. Yajuju da Majuju*
Za su fito, su sha ruwan duniya, babu wanda zai iya yakarsu sai addu'ar Annabi Isa.
*2. Zina a kan hanya*
Za a yi zina a fili a kan hanya, wanda yafi imani a lokacin shine wanda zai ce "ku dan matsa daga hanya."
*3. Wahalar wannan lokacin*
Duk wanda ya ga wannan lokacin, ba zai gama lafiya ba sai da jarrabawa mai nauyi.
*4. Shafe Al-Qur'ani*
Al-Qur'ani zai tashi daga zuciya da kuma daga takarda. Mutum zai tashi, ko Fatiha ba zai iya karantawa ba.
*5. Garuruwa sun hade ta gine-gine*
Duniya ba zata tashi ba har sai kowane gari ya hade da dan uwansa ta wajen gine-gine.
*6. Bayyanar Annabi Isa (A.S)*
Zai dawo, zai kashe Dajjal, zai karya giciye, zai kafa adalci.
*7. Fitowar Dajjal*
Mutum mai ido daya, zai yi ikirarin cewa shi Allah ne, zai yi ruwan sama da tayar da matattu a idon mutane.
*8. Dabbatul Ard*
Dabbar da zata fito daga kasa, zata yiwa mutane alama a goshi, a rarrabe mumini da kafiri.
*9. Hayaki (Dukhan)*
Hayaki zai cika duniya kwana 40, mumini yayi kamar mura, kafiri ya kumbura.
*10. Rana ta fito daga Yamma*
Ranar da rana ta fito daga yamma, tuba ba za'a karba ba daga kowa.
*11. Wuta zata koro mutane*
Wuta zata fito daga Yemen, zata koro mutane zuwa wurin Mahshar.
*12. Mata sun fi maza yawa*
Mutum 1 namiji, mata 50 suna binsa saboda karancin maza.
*13. Amana ta tashi*
Za'a bawa marar cancanta mukami, mutumin karya a gaskata shi, mai gaskiya a karyata shi.
*14. Gine-gine masu tsayi a hamada*
Makiyayan rakuma zasu yi gasa a gine-gine masu tsayi.
*15. Ilimi ya tashi*
Malamai na gaskiya su mutu, jahilai su zama shugabanni.
*16. Kisa ya yawaita*
Mutum zai kashe dan uwansa, bai san dalilin da ya kashe shi ba.
*17. Lokaci ya kankance*
Shekara ta zama kamar wata, wata kamar sati, sati kamar rana.
*18. Riba da cin haram ya zama al'ada*
Mutane ba za su damu ba ko kudin halal ne ko haram, muddin sun samu.
*19. Girgizar kasa t
2026-11-13 08:34:36
0
To see more videos from user @ansu_fati_darr, please go to the Tikwm
homepage.