@salissoukaka1: Kiwo na daga cikin muhimman hanyoyin samun kuɗin shiga ga al'ummar Jamhuriyar Nijar, musamman a yankin Maradi, inda harkokin kiwon dabbobi da kasuwancinsu ke taimaka wa iyalai wajen biyan bukatun yau da kullum. Daga cikin nau'o'in tumakin da ake kiwo, tumakin Balami suna da muhimmanci a wajen masu kiwo da 'yan kasuwa. Sai dai, yaya harkar kiwon tumakin Balami da kasuwancinsu take a Maradi? Waɗanne damammaki da ƙalubale ne ke tattare da wannan sana'a? Ga rahoton Salissou Kaka radio saraounia Maradi.#Niger #sharhin jaridun mako #AES #kiyyo#