@abbasarkii: GAJAM YA HALARCI SALLAR JANAZAR MARIGAYI HON. TASI’U MUSA A SHINKAFI, YA MIƘA TA’AZIYYARSA GA IYALAN MAMACIN Mai Girma Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta Jihar Zamfara, Mal. Abdulmalik Abubakar Gajam, ya halarci sallar jana’izar marigayi Hon. Tasi’u Musa, Kwamishinan Ma’aikatar Kasuwanci ta Jihar Zamfara, a garin Shinkafi. Kwamishina Gajam ya samu halartar jana’izar tare da takwarorinsa na Majalisar Zartarwa ta Jiha, shugabannin ƙananan hukumomi da sauran manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki, inda suka raka marigayin zuwa makwancinsa na ƙarshe. A yayin wannan babban alhini, Kwamishina Gajam ya bayyana alhininsa bisa wannan babban rashi da aka yi, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, abokan arziki da al’ummar Jihar Zamfara baki ɗaya. Ya kuma roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafarta wa marigayin, Ya jikansa da rahama, Ya haskaka kabarinsa, Ya kuma bai wa iyalansa da sauran waɗanda wannan rashi ya shafa haƙurin jure wannan babban rabo. Signed. Muhammad Ahmad Isah (Martaba) Media & Publicity Unit. Office of the Commissioner MOEST.

Abba_Sarki Visuals
Abba_Sarki Visuals
Open In TikTok:
Region: NG
Friday 13 November 2026 18:15:51 GMT
3952
417
4
59

Music

Download

Comments

sautussunnahshinkafi
umar shinkafi🫂 :
rest in peace
2026-11-13 22:20:08
0
aa.alasha7
LASHA ZAMFARA🕊🕊🕊 :
hmmm Allah sarki rayuwa Allah jikan shi da rahama
2026-11-13 21:58:44
0
user6271706074179
Deeyarh💜🌸🥰 :
Allah ymashi rahma
2026-11-13 22:45:57
0
abusadeeq273
MIJIN👸HAJIYA✅🦅001 :
[Teary eyed][Teary eyed][Teary eyed]
2026-11-14 06:55:30
0
To see more videos from user @abbasarkii, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos


About