A duk duniya ban taɓa gani ko jin wanda yayi rayuwa a duniya ya barta, kuma ya zama shi ne shugaban duniyar kamar yana raye yana rayuwa a doron ƙasa ba; sai Annabi Alaihissalam.
Duk wanda yayi magana a duniya ana tambayar hujja, amma Annabi Alaihissalam idan ya faɗi magana hujja ɗaya tak ake nema; shin shi ne ya faɗa? Ana samun tabbas shi ne ya faɗa to zance ya ƙare.
Annabi Alaihissalam shi ne Annabin Annabawa kuma Annabi mai yawan albarka