@young_politician: Kafin fara fita yakin neman zaɓe, yau a garin Hadejia, dan takarar Gwamnan Jigawa a Jam'iyyar PDP Alhaji Mustapha Sule Lamido (Santurakin Dutse) ya yi ganawa ta musamman da dukkan 'yan takarar yankin Jigawa ta Arewa Maso Gabas, shugabannin Jam'iyya na mazabu 85, shugabanni Jam'iyya na Kananan hukumomi 8 da masu ruwa da tsaki na yankin domin tattauna batutuwa masu muhimmanci da tunkarar zaɓen 2027. Muna rokon Allah ya bamu sa'a Allah ya iya mana.