@sadiq 002 :
Assalamu Alaikum wa rahmatullah, ya malam. Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya.
Na rubuto maka wannan saƙo ne domin in nuna maka godiyata da farin cikina bisa irin alherin da na samu ta hanyar bidiyon da kake wallafawa a shafinka na TikTok.
Ya malam, na yi kusan shekara biyu da aure, amma Allah bai riga ya azurta mu da samun haihuwa ba. A lokacin da nake bibiyar bidiyoyinka, na ga wani bayani da ka yi game da wani magani. Na saurara, na yi amfani da shi, Alhamdulillah, kafin cikar wata guda matata ta samu ciki.
Wallahi, ba zan iya bayyana irin farin cikin da na ji ba. Ina roƙon Allah Ya saka maka da mafificin alheri, Ya ƙara maka ilimi, lafiya, albarka da ɗaukaka. Ya sanya wannan taimakon da kake yi wa al'umma ya zama sadaka mai gudana a gare ka.
Allah Ya ba mu damar ganin wannan cikin lafiya, Ya sauƙaƙa haihuwa, Ya ba mu zuri'a saliha.
Nagode sosai, ya malam. Allah Ya saka maka da aljannatul Firdausi. Amin.
2026-11-17 22:58:42