@dalibin_rayuwa: Akwai abokan aiki, akwai abokan kasuwanci, akwai abokan karatu, akwai makwabta, akwai ’yan’uwa na jini, sannan akwai abokai da aminan da muke tattauna muhimman batutuwan da suka shafi rayuwarmu kai tsaye, waɗanda muke iya damƙa musu wasu daga cikin sirrukanmu. Dukkan waɗannan mutane suna da matsayi daban-daban a rayuwarmu. Saboda haka, akwai buƙatar mu fahimci irin alaƙar da ke tsakaninmu da kowannensu, sannan mu san irin mu’amalar da ta dace da wannan alaƙa. Ɗaya daga cikin manyan kurakuran da mutane suke tafkawa a rayuwa shi ne sanya mutane a matsayin da bai dace da su ba. Wasu suna ba abokan kasuwanci amincin da ya kamata su bai wa ’yan’uwansu na jini. Wasu kuma suna ɗaukar abokan aiki a matsayin abokan sirri, har su riƙa bayyana musu abubuwan da bai kamata su sani ba. Abokin kasuwanci ko abokin aiki, abokin neman arziki ne. Ku girmama yarjejeniyarku, ku kiyaye haƙƙoƙin juna, sannan ku gudanar da al’amuranku bisa doron gaskiya da adalci. Amma kada kusancin da ke tsakaninku ya sa ka manta cewa kowannenku yana da nasa muradin da yake son cimmawa. Akwai gasa, akwai bambancin ra’ayi, akwai kuma yiwuwar hassada ta gifta a tsakaninku. Saboda haka, dole ne ka kasance mai fahimtar kowane motsi na abokin mu’amalarka. Haka ma makwabta, ’yan’uwa da abokan zamantakewa. Kowannensu yana da haƙƙoƙi da iyakokin da ya kamata a kiyaye. Ko da babu wata alaƙa ta jini, to lallai akwai mutanen da ya kamata ka kusanto da su kusa dakai saboda tasirinsu ga ci gaban rayuwarka. Haka zalika, akwai waɗanda amanar su za ta sa ka iya damƙa musu sirrinka. Sannan akwai waɗanda ya fi dacewa ku ci gaba da yi wa juna fatan alheri daga nesa, ko da kuwa sun kasance shaƙiƙanka. Allah Ya sa mu dace. #Abdulfatah_yakubu #Dalibin_rayuwa
DALIBIN RAYUWA
Region: NG
Wednesday 18 November 2026 19:54:41 GMT
Music
Download
Comments
Naira Marley :
guarantee
2026-11-19 14:14:50
1
baseer :
muna gdy
2026-11-19 16:30:20
1
RCHP SUFIYANU LAWAL ✅💊 :
@RCHP SUFIYANU LAWAL ✅💊:Ba da kowa Ake kulla Alaka mai Dogon zango ba.wasu mutanen Yafi dacewa kuci gaba da yiwa juna Fatan Alkairi daga nesa 🙏👌
2026-11-18 22:17:27
2
@.Promise :
wannan gaskiya ne bro
2026-11-18 23:01:07
1
SAHABI KT :
wanan Hakan yake
2026-11-18 21:29:46
1
𝐑𝐈𝐉𝐀𝐋𝐔_𝐂𝐎𝐍𝐂𝐄𝐏𝐓✅ :
Allah yasaka da Alkhairi
2026-11-18 20:00:36
1
Sadiq :
hmm kai dai Bari Dan uwa😥😥
2026-11-19 20:41:59
0
A _B🌹S K T✊ :
wannan gaskiya ne
2026-11-19 21:24:45
0
ABBA APE 💙🦅 :
Wannan haka yake bro 😭😭
2026-11-19 17:58:48
0
DAN BAABA CT TEX✅ :
muna sai da Shadda, yard, men lace. Etc
2026-11-18 22:20:59
1
🧡Mr_INNOCEN🩶 :
🫵🏻🫵🏻💯☑️🫡🫡🫡
2026-11-19 15:22:21
0
To see more videos from user @dalibin_rayuwa, please go to the Tikwm
homepage.