@yarfulanigombe7: Ya Allah, Ka tsare min yayata a duk inda take. Ka ba ta lafiya mai ɗorewa, farin ciki da kwanciyar hankali. Ka nisantar da ita daga dukkan sharri da damuwa. Ka buɗe mata ƙofofin arziki da nasara. Ka biya mata dukkan buƙatunta na alheri, Ka tsawaita rayuwarta cikin imani da albarka. Ya Allah, duk inda take, Ka kasance tare da ita. Ka sa duniya ta yi mata kyau, lahira ma ta yi mata kyau. Ina sonki sosai Yayata. Allah Ya ƙara miki albarka. ❤️🤲 آمين.