@lele_4real: YANZU-YANZU: Fitaccen malamin nan Sheikh Ahmad Gumi ya nemi a cire duk wani sarki da aka samu da aikata rashin da’a. Sheikh Ahmad Gumi ya yi kira da a cire duk wani sarki da aka samu da aikata rashin ɗa’a, a yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan zargin cin zarafin wata mata da ake yi wa Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Zargin ya biyo bayan wata baƙuwa yar yawon buɗe ido daga ƙasar waje da ta bayyana cewa, a lokacin ziyararta fadar Sarkin Daura ranar 14 ga watan Nuwamba, sarkin ya riƙe hannunta, ya rungume ta sannan ya sumbace ta a kumatu. Matar, wacce aka fi sani da @beduinqa a Instagram, ta kasance tana gudanar da rangadin ziyartar ƙasashe 197 na duniya, inda Najeriya ta kasance ƙasa ta 184 a cikin jerin ƙasashen da take ziyarta. Lamarin ya haifar da muhawara mai zafi a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama ke bayyana ra’ayoyinsu kan zargin da kuma kira da a tabbatar da gaskiyar lamarin. Daga lele4real
𝙻𝙴𝙻𝙴
Region: NG
Sunday 22 November 2026 21:28:25 GMT
Music
Download
Comments
Hamisu nejar :
🥰🥰
2026-11-22 23:13:23
0
salisu hamisu :
🥰🥰🥰
2026-11-22 21:33:08
1
MOUBARA.M.K.D :
😁😁😁
2026-11-22 22:56:13
0
Ismail mb :
🥰🥰🥰
2026-11-23 06:14:23
0
2026octoba :
🥰🥰🥰
2026-11-23 09:28:16
0
To see more videos from user @lele_4real, please go to the Tikwm
homepage.