𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍-𝑮𝒂𝒎𝒆𝒔𝒆𝒏𝒔𝒆 :
Wallahi, ji nake kamar na faɗi na mutu saboda tsananin baƙin ciki. Abin da ya fi karya min zuciya shi ne ganin wai Hausawa, mu ne muka fi yaɗa wannan bidiyon.
Ko da ace abin da ake zargi gaskiya ne, ya kamata mu tuna cewa mutum ba Annabi ba ne; kowa yana da kuskuren da ya taɓa aikatawa, wanda bai kamata a mayar da shi abin kunyatawa da wulaƙanta shi a gaban duniya ba.
Al’adarmu ta Hausawa al’ada ce ta mutunci, kunya, tausayi, sutura da kare martabar juna. Ya kamata mu kasance masu rufe aibin mutane, ba masu tona shi da yaɗa shi ba.
Wallahi, idan wannan ba wani shiri ne na ƙirƙira ko set-up ba, to me ya sa aka yi recording ɗin da wannan gilashin, aka adana shi, sannan aka yaɗa shi? Me ya sa ba a bar abin a tsakaninsu ba, maimakon a mayar da shi abin magana a duniya?
Abin da ya fi min ciwo ba wai kawai abin da ya faru ba ne, amma yadda muka manta da mutuncinmu, muka zama masu gaggawar yaɗa abin kunya, alhali muna da damar zaɓar shiru, tausayi da kare martabar ɗan’uwanmu.
Ba duk abin da muka gani ne ya kamata mu yaɗa ba. Ba duk kuskuren mutum ne ya kamata ya zama abin hukunta shi a gaban duniya ba.
Allah Ya kiyaye mana mutuncinmu, Ya sa mu zama masu suturta juna, Ya kuma shiryar da mu zuwa ga abin da ya fi alheri. 🤍
2026-11-23 20:58:35