@hussainimuhd42: CHAIRMAN YA KORI WASU FULANI 'YAN GUDUN HIJIRA DAGA CIKIN GARI Chairman na Karamar Hukumar Sakaba da ke Jihar Kebbi ya yanke shawarar korar wasu Fulani 'yan gudun hijira daga cikin garin Sakaba, bisa zargin cewa suna ɓoye 'yan uwansu Fulani masu alaƙa da 'yan bindiga. A cewarsa, duk lokacin da aka sanya ranar tantance waɗannan mutane domin sanin asalinsu da inda suka fito, da yawa daga cikinsu ba sa zuwa. Wannan lamari ya jawo damuwa kan tsaron al'ummar Sakaba, musamman ganin cewa ana zargin wasu daga cikin waɗannan mutane da yiwuwar kasancewa da alaƙa da masu aikata laifuka. Chairman ɗin ya bayyana cewa waɗanda suka sayi gidaje za a biya su kuɗinsu, sannan waɗanda suke haya za a biya su kuɗin hayarsu, amma dole ne su bar garin. Muna kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da, sun gudanar da bincike bisa doka, sannan su ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda aka tabbatar yana taimaka wa 'yan bindiga. Tsaron Sakaba yana da muhimmanci, kuma duk wanda yake taimaka wa masu aikata laifuka ya kamata ya fuskanci hukuncin da doka ta tanada. Allah Ya kawo ƙarshen rashin tsaro a Sakaba da Jihar Kebbi baki ɗaya. #foryou #fyp #viral #fypシ #foryoupage
HMNG
Region: ES
Thursday 26 November 2026 09:09:30 GMT
Music
Download
Comments
𝑺𝑰𝑹𝑫𝑬𝑬𝑸 🤪 :
💪💪💪
2026-11-26 09:29:08
0
To see more videos from user @hussainimuhd42, please go to the Tikwm
homepage.