@auwal.mohd1: Makiya Kwankwasiyya Ta Ina zaku fara ne Nan fa Kudancin Nigeria ne.... Kwankwaso ajiyar Allah..... Wani taimako da gata da Allah yakewa Jagora Eng. Sanata Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso, a duk sadda maƙiyansa suka buɗe baki da nufin su tozarta shi, sai ƙahriyyar Allah ta bashi garkuwa daga sharrinsu. Sai sharrin na su ya koma yabo ko ƙarin farin jini a gare shi. 1- Bayan sun lalata masa jam'iyya (NNPP) sun ƙirƙira mata rigingimun cikin gida dan su ba wa kansu hujjar butulce masa, sun fita sun koma APC tare da iƙrarin sun ƙwacewa Jagora "Structure" amma a taronsu na farko Allah ya kunyata su suka dawo suna zargin juna dan ganin ba su da kowa. Structure ɗin da suka ce sun ƙwace masa, ashe tana tare da shi. 2- Rarara yai musu waƙa yana cin mutuncin Sanata Kwankwaso, sukai taro suka ɗebo mata ƴan tasha da ƴan kwalta suna ɗaga Ɗankamfai akan titi, da nufin cewar na Jagora Kwankwaso ne dan ci masa mutunci, amma a ƙasa da 24hrs Allah ya mai da musu da sharrin kansu, aka dinga cewa gwamnatin Kano tai empowerment na Ɗankamfai. Kan ka ce me sun dawo suna faɗin haƙiƙar abun da sukai cewar sun yi ne dan cin mutuncin wanda yai musu riga da wando, nan ma suka kuma daɓawa kansu wuƙa. Suka ma rasa ta yadda za si damage control ɗin. Ba za su iya faɗar gaskiya ba, kuma ƙaryar ba za ta yiwu ba. 3- Bayan turka-turkar da ta faru da gwamna Abba da matarsa, ɗiyar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, saboda ta je kotu ta nemi saki, Abba ya fito kan teburin siyasa ya ci mutuncinta da na Jagora Kwankwaso, har da iƙirarin zai buɗe Portal na zaɓar mata mai mutunci ƴar mutunci, a ƙoƙarinsa na nuna cewar matarsa da ya haifa masa yara har 6, ba mai mutunci bace ba ƴar mutunci bace. Ƙarshe wannan abun ma Kwankwaso ya ƙara janyowa masoya, domin sanin da sukai kan alaƙar Kwankwason da Abba, kuma yai masa wannan tozarcin. Ya nuna lallai Rasdan bai gaji arziƙi ba, anan duk mata masu mutunci suka ce ti fa ba sa su zaɓi wanda zai tozarta matarsa a idon duniya ba. 4- Suka zo suka kai Jagora Kwankwaso EFCC wai ta bincike shi, har suna iƙirarin wai Kwankwaso ya fi kowanne shugaba sintiri a wannan hukuma, amma kuma hukumar ba ta taɓa kama shi da laifi ta kai shi kotu ba. Wannan abun ba ƙaramin tsarkake Kwankwaso yai ba, da nuna cewar shugaba ne shi mai amana da bai handama da babakere da dukiyar al'uma ba. Domin da idonmu muma ganin shugabannin da sau ɗaya EFCC ta bincike su, amma sun dangana da kotu, wasu har da prison. Wannan ya nuna Kwankwaso amintaccen Jagora ne. Note:- Ba kowanne bawa yake samun irin wannan taimakon daga Allah ba sai wanda Allah ya zaɓa, maƙiyanka su zama su ne zugazugin ɗaukakarka. Tabbas lamarin Kwankwaso lamarin Allah ne. 29/nNovember/2026 private life Medea TV ✍️ #nigeriapolitics #ok #arewa__tiktok #foryoupage #fypシ゚viral

P.R.I.V.A.T.E L.I.F.E backup✍️
P.R.I.V.A.T.E L.I.F.E backup✍️
Open In TikTok:
Region: NG
Sunday 29 November 2026 05:45:17 GMT
7260
1540
12
40

Music

Download

Comments

user392087065
Usman Muhammad :
kwankwasiyya
2026-11-29 12:55:20
0
ibrahimkhalilro1
Baba Iro :
Yan kwankwasiya Kano kuyi gwarzo Amma sama kuyi Atiku wnn shine
2026-11-29 13:19:17
0
sj.jd856
CEO :
2026-11-29 10:08:06
1
jesssymamajay
MamaJay :
2026-11-29 13:17:12
0
jamiluabdullahi03
jamiluabdullahi03 :
2026-11-29 10:15:22
0
musleembig
مسلم امس كلوت✂️🇳🇬 :
Falle dayache
2026-11-29 12:30:36
0
dan.mama3393
EL GAY :
👌👌👌
2026-11-29 12:34:27
1
ibraheemabdultudu
Comrd. Ibraheem Abdul Tudunwad :
👍👍👍
2026-11-29 12:15:19
1
ibrahimsani7637
Ibrahim Sani :
🥰🥰🥰
2026-11-29 12:42:06
1
hassan.ibrahim8567
HASSAN IBRAHIM :
🥰🥰🥰🥰🥰🥰
2026-11-29 08:37:25
1
abubakarsabiu6
A.sadeek88 :
👍👍👍
2026-11-29 09:50:30
1
alhaji.moukur
alhaji moukur :
🥰🥰🥰
2026-11-29 07:29:46
1
annoorr_phone_stare
ANNOORR_PHONE-STORE :
🥰🥰🥰
2026-11-29 07:46:42
1
saminu_dan_kasa
Dan kasa :
👑👑👑
2026-11-29 08:59:44
1
salisudubey
Salisu Dubey :
🥰🥰🥰
2026-11-29 09:30:44
0
yusufgold789
Yusufgold :
🥰🥰🥰
2026-11-29 10:43:58
0
khaleefa3079
J M J F :
🥰🥰🥰
2026-11-29 10:45:53
0
user.mahammadu
bamala💚💚🫂✌️ :
👈👈👈
2026-11-29 11:36:29
0
inusamk01
íñűšà mķ🤴 :
🥰🥰🥰
2026-11-29 12:41:01
0
To see more videos from user @auwal.mohd1, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos


About