@mypspace9208: 26.06.28 5 cm 🎥 @Zloty เพราะมาก 5 cm. ที่คิดถึง WILLIAM PVM SKIN CLASS #ProvamedxWilliam #williamjkp

MyPSpace 🧸🍠✨
MyPSpace 🧸🍠✨
Open In TikTok:
Region: TH
Sunday 28 June 2026 13:02:58 GMT
676
98
2
4

Music

Download

Comments

sainawalert
ทรายแมวววว :
สุดหล่อของหม่าม้า
2026-06-30 13:11:38
0
akimanang5785
Aki Manang1988 :
เพราะมาก
2026-06-29 06:01:43
0
To see more videos from user @mypspace9208, please go to the Tikwm homepage.

Other Videos

Akwai abokan aiki, akwai abokan kasuwanci, akwai abokan karatu, akwai makwabta, akwai ’yan’uwa na jini, sannan akwai abokai da aminan da muke tattauna muhimman batutuwan da suka shafi rayuwarmu kai tsaye, waɗanda muke iya damƙa musu wasu daga cikin sirrukanmu. Dukkan waɗannan mutane suna da matsayi daban-daban a rayuwarmu. Saboda haka, akwai buƙatar mu fahimci irin alaƙar da ke tsakaninmu da kowannensu, sannan mu san irin mu’amalar da ta dace da wannan alaƙa. Ɗaya daga cikin manyan kurakuran da mutane suke tafkawa a rayuwa shi ne sanya mutane a matsayin da bai dace da su ba. Wasu suna ba abokan kasuwanci amincin da ya kamata su bai wa ’yan’uwansu na jini. Wasu kuma suna ɗaukar abokan aiki a matsayin abokan sirri, har su riƙa bayyana musu abubuwan da bai kamata su sani ba. Abokin kasuwanci ko abokin aiki, abokin neman arziki ne. Ku girmama yarjejeniyarku, ku kiyaye haƙƙoƙin juna, sannan ku gudanar da al’amuranku bisa doron gaskiya da adalci. Amma kada kusancin da ke tsakaninku ya sa ka manta cewa kowannenku yana da nasa muradin da yake son cimmawa. Akwai gasa, akwai bambancin ra’ayi, akwai kuma yiwuwar hassada ta gifta a tsakaninku. Saboda haka, dole ne ka kasance mai fahimtar kowane motsi na abokin mu’amalarka. Haka ma makwabta, ’yan’uwa da abokan zamantakewa. Kowannensu yana da haƙƙoƙi da iyakokin da ya kamata a kiyaye. Ko da babu wata alaƙa ta jini, to lallai akwai mutanen da ya kamata ka kusanto da su kusa dakai saboda tasirinsu ga ci gaban rayuwarka. Haka zalika, akwai waɗanda amanar su za ta sa ka iya damƙa musu sirrinka. Sannan akwai waɗanda ya fi dacewa ku ci gaba da yi wa juna fatan alheri daga nesa, ko da kuwa sun kasance shaƙiƙanka. Allah Ya sa mu dace. #Abdulfatah_yakubu #Dalibin_rayuwa

About