@malamin.rayuwa0: SHIN LAFIYARKA LAU KUWA? Maza suna can suna fafutukar buɗe sabbin kasuwanci, mallakar kadarori, neman ilimi na addini, boko da fasaha, kafa kamfanoni, gina madogarar arziƙi mai karko, da kuma samar da mafita ga matsalolin rayuwar iyalansu a nan gaba. ............ Alhalin kai kuma ka shagaltu da koyon yadda zaka riƙa tausasawa mace murya don kawai ta so ka ko ta aure ka. ........... Alhalin kai kuma ka shagaltu da ɓata sa'o'i kana faɗa da zagi a shafukan sada zumunta don kare ɗan siyasa, mawaƙi, ko ɗan ƙwallon da bai ma san kana numfashi a doron ƙasa ba. ............ Alhalin kai kuma ka shagaltu da lissafin wanda ya kalli hoto ko rubutun da ka ɗora a wayarka bai ce komai ba, ko ɗaukar zafi a zuciya don kawai wata ta karanta saƙonka amma ta ƙi ba ka amsa da wuri. ............ Alhalin kai kuma ka shagaltu da ƙwarewa wajen kukan tsadar rayuwa, yawan mita, da ɗora laifin talaucinka a kan ƙaddara kana jiran wani ya zo ya cece ka a cikin ɗakinka. Ɗan'uwa, shin lafiyarka lau kuwa? Don Allah mu gyara......
👳MALAMIN RAYUWA!!!!!😔
Region: NG
Saturday 08 August 2026 19:14:32 GMT
Music
Download
Comments
There are no more comments for this video.
To see more videos from user @malamin.rayuwa0, please go to the Tikwm
homepage.