DAN KANI ABAYA :
Wallahi, zafin rasa uwa ba ya misaltuwa. Uwa ba kawai mutum ba ce a rayuwar ɗanta; ita ce mafaka, addu'a, tausayi da nutsuwar zuciya. Ranar da ta tafi, kamar wani ɓangare na rayuwarka ne ya tafi tare da ita. Akwai kewar da ba hawaye ne kawai ke bayyana ta ba, akwai lokacin da zuciya take buƙatar jin muryarta, ta ji addu'arta, ko ta kira ta da kalmar Mama, amma sai ka tuna cewa ba za ka ƙara ganinta a duniya ba. Abin da ya rage mana shi ne addu'a da kyakkyawan fata ga Allah. Allah Ya jiƙan mahaifiyata, Ya gafarta mata, Ya yalwata kabarinta, Ya haskaka mata shi, Ya ba ta Aljannatul Firdaus. Allah Ya haɗa mu da ita a gidan Aljanna, inda babu rabuwa kuma babu kuka. 😭🤲💔
2026-11-24 12:34:30